Faransa-Coronavirus

Tsanantar corona ta tilasta sake sanya dokar takaita walwala a Faransa

Shugaba Emmanuel Macron tare da ministan lafiya na Faransar Olivier Véran.
Shugaba Emmanuel Macron tare da ministan lafiya na Faransar Olivier Véran. AP - Ludovic Marin

Ma’aikatar lafiyar Faransa ta bayyana fargabar harbuwar Karin tarin jama’ar kasar da Coronavirus dai dai lokacin da aka fara aiwatar da sabuwar dokar takaita zirga zirga a sassan kasar don dakile yaduwar cutar.

Talla

Ministan lafiya Olivier Veran yayi hasashen cewar cutar zata karu a tsakiyar wannan wata na Afrilu, yayin da za a cigaba da samun karuwar mutanen da za a kwantar a asibiti zuwa karshen wata.

Daraktan asibitin Antony da ke Paris, Denis Chandesris yace sun kara gadajen asibitin a bangaren gobe da nisa wajen sallamar mutanen da rashin lafiyar su bai yi tsanani ba domin baiwa masu fama da cutar damar samun gadon kwanciya.

A makon jiya wata tawagar ma’aikatar lafiya ta yi gargadi a budadiyar wasika ga hukumomin Faransa dangane da sake samun karuwar cutar.

 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.