Turkiya-EU

Tarayyar Turai ta ja kunnen Erdogan kan muhimmancin hakkin dan adam

Shugaba Recep Dayyib Erdogan yayin karbar bakoncin shugabannin EU Charles Michel da Ursula von der Leyen a Ankara.
Shugaba Recep Dayyib Erdogan yayin karbar bakoncin shugabannin EU Charles Michel da Ursula von der Leyen a Ankara. via REUTERS - PRESIDENTIAL PRESS OFFICE

Shugabannin Kasashen Turai da ke ziyarra Turkiya sun bayyana damuwar su kan abinda suka kira take hakkin Bil Adama da akeyi a kasar, yayin da suke bayyana fatar samun dangantaka mai dorewa a tsakanin su bayan ganawa da shugaba Recep Tayyip Erdogan.

Talla

Jami’an kasashen Turai sun ce shugaban majalisa Charles Michel da shugabar gudanarwa Ursula von der Leyen na bukatar gabatarwa shugaba Erdogan bukatun su da suke so bangarorin biyu sun amince domin samun dangantaka mai karfi.

Bayan kwashe sa’oi 3 suna ganawa, von der Leyen ta shaidawa manema labarai cewar sun jaddadawa Erdogan cewar ba zasu daga kafa kan batun ‘yancin Bil adama ba.

Ziyarar shugabannin na EU na da shirin gyatta alakar da ke tsakanin kungiyar da Turkiya wadda ke a baya ke da kudirin zama mamba a Tarayyar ta Turai amma kuma rikice-rikicen da ke tsakaninta da kasashe mambobin kungiyar da ma batun take hakkin dan adam ya hana cimma muradun kasar.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI