Lafiya

Kotun Turai ta yi umarnin tilastawa iyalai karbar rigakafin yara

Wannan ne karon farko da kotun ke zartas da makamancin hukuncin, wajen tilasta karbar rigakafin.
Wannan ne karon farko da kotun ke zartas da makamancin hukuncin, wajen tilasta karbar rigakafin. JOE RAEDLE / GETTY IMAGES NORTH AMERICA / AFP

Kotun kare hakkin Dan Adam ta Tarayyar Turai, ta zartas da hukuncin tilastawa kowanne iyalai da ke cikin kasar mai bin tsarin Demokradiyya karbar alluran rigakafin da ake yiwa kananan yara na ka'ida, dai dai lokacin da coronavirus ke ci gaba da barazana ga Lafiya.

Talla

Kotun ta ECHR wadda wannan ne karon farko da ta zartas da makamancin hukuncin na tilastawa Iyalai bai wa 'ya'yansu rigakafin wajibi da aka saba don bayar da cikakkiyar kariya ga lafiyarsu, ta ce matakin tilasta baiwa yara rigakafin bai saba da tanadin sashe na 8 na kundin kare hakkin dan adam na tarayyar Turai ba.

Hukuncin Kotun na yau Alhamis na zuwa ne bayan wasu Iyalai sun garzaya gabanta don neman hana matakin mahukuntan jamhuriyyar Czech da ta tilasta yiwa kananan yara rigakafin da aka saba yi musu don basu kariya.

Karkashin dokokin Jamhuriyyar Czech kowanne yaro wajibi ne ya karbi rigakafin kariya daga cutukan 9 da ke barazana ga kananan yara  da suka kunshi, ciwon hanta, kyanda, tari da kuma ciwon makogwaro da ma cutar da ake samu jikin tsatsa wato ''tetanus''.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.