Faransa-Lafiya

Kudirin halasta kashe marasa lafiya ya haddasa rarrabuwar kai a Faransa

Spain ita ce kasar Turai ta baya-bayan nan da ta amince da kudirin zuwa doka bayan Belgium, Luxembourg da Switzerland.
Spain ita ce kasar Turai ta baya-bayan nan da ta amince da kudirin zuwa doka bayan Belgium, Luxembourg da Switzerland. Europa Press via Getty Images - Europa Press News

An samu rarrabuwar kawuna a Majalisar Dokokin Faransa dangane da kudirin da ke neman halasta saukakawa marasa lafiya mutuwa, kudirin da mambobin Majalisar ke shirin kadawa kuri’a bayan tafka muhawara akai.

Talla

Manyan mukarraban gwamnatin Faransa da shi kansa shugaba Emmanuel Macron na cikin ‘yan gaba gaba da ke goyon bayan zartas da kudirin zuwa doka, don saukakawa marasa lafiyan da ke fama da cutar da bata warkewa mutuwa cikin sauki.

Kafin yanzu dai Faransa na amfani da nau’ikan magunguna kashe jiki da gusar da hankali ne kan masu irin wannan cuta da bata da magani kuma suke cikin mawuyacin hali tsawon lokaci, sabanin wasu kasashe da ke amfani da dokar saukakawa masu irin cutukan mutuwa a saukake ko kuma kashesu a cikin salama.

A cewar Olivier Falorni na jam’iyyar masu matsakaicin ra’ayi, zartas da dokar za ta saukakawa dubunnan Faransawan da ke tsallakawa Belgium ko Switzerland don samun taimakon saukaka musu mutuwa.

Matukar dai masu goyon bayan kudirin suka samu rinjaye a Majalisar kenan Faransa za ta zamo kasar Turai ta 5 da ta zartas da dokar ta taimakawa mutane mutuwa bayan Netherlands da Belgium da Spain da kuma Luxembourg.

Dan Majalisa Falorni da ke bayyana muhimmancin amincewa da kudirin zuwa doka, ya ce a duk shekara likitocin Faransar a boye na kashe marasa lafiya akalla dubu 2 zuwa dubu 4 don saukaka musu daga cutar da suke fama da ita.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.