Faransa-Siyasa

Tsohon Firaministan Faransa na barazana ga Macron

Edouard Philippe tare da shugaba Emmanuel Macron
Edouard Philippe tare da shugaba Emmanuel Macron © CHRISTIAN HARTMANN / POOL / AFP

Tsohon Firaministan Faransa Edouard Philippe na shirin tsayawa takara a zaben shugaban kasar mai zuwa, abin da ake kallo a matsayin wata barazana ga shugaba Eammanuel Macron a siyasance.

Talla

Philipe shi ne Firaministan da shugaba Macron ya nada a farkon mulkinsa, inda kuma ya shafe shekaru uku yana rike da wannan mukami kafin daga bisani ya ajiye aikinsa.

Bayan ajiye mukamin nasa, Philippe ya kuma fice daga jam’iyya mai mulkin kasar ta Macron tare da komawa jam’iyyar hamayya wadda karkashinta ne zai  tsaya takarar don kalubalantar tsohon ubangidansa.

Masharhanta kan siyasa a kasar na ganin cewa, Philippe ka iya zama babbar barazana ga Macron a yayin zaben, kasancewar Macron din ya amince masa matuka lokacin da yake Firaministan.

A zamanin da yake rike da mukamin siyasa ,Philippe shi ne shugaban Hukumar Kula da ‘Yan Fansho ta kasar, kuma ya taka rawar gani matuka.

A baya, al’umma na ganin watakila Philippe ya hakura da siyasa ne la’akari da yadda aka ji shi shiru na tsawon watanni tara.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI