Italia-mafia

'Yan sandan Italiya sun kame batagari 50 kan kaucewa biyan haraji

Jami'an 'yansandan Italiya bayan wani sumame.
Jami'an 'yansandan Italiya bayan wani sumame. AP - Valeria Ferraro

Wani sumamen jami’an tsaro a Italiya ya kai ga kame batagari akalla 50 baya ga tsabar kudi yuro biliyan 1 biyo bayan wata damfara da kungiyar tsagerun Ndrangheta ta yiwa gwamnati a bangaren hada-hadar man fetur, damfara mafi muni da aka gani a baya-bayan nan.

Talla

Gomman mutane aka kame daga jiya Alhamis zuwa yau karkashin sumamen jami’an ‘yansandan na Italiya da aka yiwa lakabi da ‘‘Operation PetrolMafias’’wanda ke biyo bayan badakalar da ta dabaibaye karkatar da kudaden harajin bangaren mai cikinsu har jagororin kungiyar tsagerun ta Ndrangheta.

Kungiyar tsagerun wadda ta yi kaurin suna wajen babakere da damfara a yankunan Camorra da Calabrian na kasar tuni jami’an tsaron Italiyan suka kwace manyan kadarorinta bayan fallasuwar badakalar man da kuma kaucewa biyan haraji na tsawon lokaci.

Wasu bayanai da jami’an tsaron na Italiya suka wallafa sun ruwaito yadda aka samu gibin harajin tsabar kudi yuro miliyan 173 a bangaren mai daga 2015 zuwa yanzu a yankunan kasar da kungiyar ke da tasiri da suka kunshi, Naples da Rome da kuma Calabria.

Akalla jami’an ‘yansanda dubu guda ke cikin aikin sumamen na bazata da ya kai ga kame ‘ya’yan kungiyar 50, da ke da hannu a badakalar man da kuma kaucewa biyan haraji.

Sashen ‘yan sandan Italiya ya ce kungiyar ta Ndrangheta ta yi takardun haraji na bogi, a kamfanonin manta 12 da Depo 5 da tashoshin gas 37 tsakanin 2018 zuwa 2019 wanda ya kai ga gibin yuro miliyan 5 da dubu dari 8 a harajin da ya kamata su biya gwamnatin kasar.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.