Rasha-Jamus

Putin da Merkel sun gana kan rikicin Ukraine

Merkel da Putin
Merkel da Putin REUTERS/Maxim Zmeyev

Shugaban Rasha Vladmir Putin da shugabar gwamnatin Jamus Angela Markel sun nuna takaicinsu kan rikicin gabashin Ukraine, yayin da suka tattauna kan jagoran ‘yan adawar Rasha Alexie Navalny.

Talla

Wannan na zuwa ne a daidai lokacin da rikici ya barke tsakanin ‘yan awaren Ukraine da ke samun goyon bayan Rasha.

Shugabannin biyu sun tattauna ne da nufin lalubo hanyoyin magance wannan matsalar, kafin ta kara yaduwa cikin wasu sassan kasar.

Sanarwar da fadar Kremlin ta fitar, ta ce shugabannin kasashen biyu sun ce, akwai bukatar a yi gaggawar dakatar da wannan rikici na gabashin Ukraine, inda suka ce, matukar ba a dauki matakin da ya dace a kan lokaci ba, to kuwa rikicin zai iya zafafa.

Sai dai kuma Putin ya bayyana takaicinsa kan irin matakan da Ukraine ke dauka masu ban haushi, yana mai cewa shi ne ma dalilin da ya sa rikicin ke kara zafafa.

A baya-bayan nan, shugaban Ukraine Volodymyr Zelensky ya ziyarci yankin da ke fama da rikicin, inda ya bukaci taikamon kasashe kawayen kasar don magance shi.

Wannan rikici ya fara ne tun a 2014 bayan da Rasha ta yi yukurin mamaye wani yanki na Ukraine, rikicin da ya yi sanadiyar mutuwar mutane sama da 13,000

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.