Faransa-Hari

Wani mahari ya bude wuta kan asibitin Paris

An girke jami'an tsaro a harabar asibitin  da aka kai hari a birnin Paris na Faransa
An girke jami'an tsaro a harabar asibitin da aka kai hari a birnin Paris na Faransa AFP/File

Wani mahari ya bindige mutun guda har lahira tare da jikkata wata mata a harabar asibitin birnin Paris na Faransa kafin ya tsere a kan babur kamar yadda jami’an ‘yan sanda suka sanar.

Talla

Maharin da ba a fayyace shi, ya harba harsashai da dama a asibitin na Henry Dunant mai kula da gajiyayyu wanda ke karkashin kulawar Kungiyar Agaji ta Red Cross.

An garzaya da mutanen da lamarin ya shafa zuwa asibiti, amma tuni mutumin ya mutu saboda munanan raunukan  harsashai da ya samu a jikinsa.

Kawo yanzu babu cikakkiyar masaniya game da makasudin kaddamar da farmakin, yayin da jami’an 'yan sanda suka killace harabar asibitin.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.