Faransa - Cote d'Ivoire

Kotun Faransa ta yankewa wasu sojoji haya daurin rai da rai

Wani sojan Faransa a gaban wata makaranta dake birnin Bouaké, ranar 10 ga Nuwamban 2004.
Wani sojan Faransa a gaban wata makaranta dake birnin Bouaké, ranar 10 ga Nuwamban 2004. © AFP - Philippe Desmazes

Wata Kotu a Faransa ta yankewa wani sojin hayan Belarus da wasu sojojin Cote d’Ivoire biyu hukuncin daurin rai da rai saboda samun su da laifin bude wuta kan sansanin sojin kasar dake Bouake a shekarar 2004, abinda yayi sanadiyar mutuwar mutane 10.

Talla

An yiwa mutanen 3 shari’ar ce a bayan idan su, kuma sun kunshi Yury Sushkin, direban jirgin saman sojin da ya kai harin, da wasu takwarorin sa biyu yan kasar cote d’Ivoire Patrice Ouel da Ange Gnanduillet.

Rahotanni sun ce a ranar 6 ga watan Nuwambar shekarar 2004 jirgin saman yaki yabi ta kan sansanin sojin Faransa inda ya harba makamin roka da ya kasha 9 daga cikin su da wani BaAmurke guda, yayin da wasu mutane 40 suka jikkata.

An kai harin ne a daidai lokacin da tsohon shugaban kasa Laurent Gbagbo ke kokarin kakkabe yan tawayen da suka mamaye yankin arewacin kasar tun daga shekarar 2002.

Dangantaka tsakanin Faransa da Cote d’Ivoire ta tabarbare, abinda ya haifar da zanga zangar adawa da ita a kudancin kasar, matakin da ya tilasatawa gwamnatin Faransa kwashe dubban yan kasar ta daga Cote d’Ivoire.

Wasu na kusa da shugaba Gbagbo sun ce jirgin ya dauki sansanin sojin Faransa a matsayin wani dandalin yan tawaye ne.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.