Rasha - Ukraine

Faransa da Jamus sun bukaci janyewar dakarun Rasha daga iyakar Ukraine

Mayakan 'yan awaren gabashin kasar Ukraine da Rasha ke marawa baya a yanin Petrivske.
Mayakan 'yan awaren gabashin kasar Ukraine da Rasha ke marawa baya a yanin Petrivske. AP - Alexei Alexandrov

Shugaban Faransa Emmanuel Macron, Angela Merkel shugabar gwamnatin Jamus da kuma Firaministan Ukraine Denys Shmyhal sun bukaci Rasha ta rage yawan dakarun da ta girke akan iyakarta da kasar ta Ukraine, da zummar kawo karshen zaman tankiyar dake neman haddasa barkewar sabon yaki tsakanin kasashen 2.

Talla

Shugabannin uku sun yi wannan kira ne cikin sanawar bayan taron da suka yi a yau Juma’a, inda suka gana kan halin da ake ciki dangane da rikicin Ukraine da mayakan ‘yan awaren kasar da Rasha ke marawa baya.

A kokarin kaucewa barkewar sabon yaki ne kuma, yayin ganawar ta yau, shugaban Ukraine Volodomyr Zelensky ya bukaci gudanar da taron sulhu na kai tsaye tsakaninsa da takwaransa na Rasha Vladimir Putin, a karkashin jagorancin shiga tsakanin Emmanuel Macron na Faransa da shugabar gwamnatin Jamus Angela Merkel.

Wasu mazauna yankin 'yan aware dake gabashin kasar Ukraine, yayin duba yadda ruwan bama bamai ya ragargaza muhallinsu a yankin Donetsk.
Wasu mazauna yankin 'yan aware dake gabashin kasar Ukraine, yayin duba yadda ruwan bama bamai ya ragargaza muhallinsu a yankin Donetsk. AP

Zaman tankiyar da ya karu akan iyakokin Ukarine da Rasha daga yankunansu na arewaci da gabashi, da kuma yankin Crimea da Rashar ta mamaye a shekarar 2014,  na zuwa ne a daidai lokacin da arrangama ke karuwa tsakanin sojojin Ukraine da ‘yan aware masu samun goyon bayan Rasha, rikicin da kakakin shugaba Putin Demitry Peskov ya zargi gwamnatin Ukraine da soma tsokanowa, tare da bukatar ta gaggauta komawa mutunta yarjejeniyar tsagaita wutar da aka cimma a watan Yuli.

Sai dai Ukraine ta zargi Rasha ta yi mata barazana da yaki, matakin da tace za ta yiwa raddi da karfin soja.

Daga farkon shekarar da muke zuwa yanzu sojojin Ukraine akalla 20 ne suka rasa rayukansu, sabanin 50 a tsawon shekarar 2020, yayin gwabza fada da ‘yan awaren Rasha.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI