Rasha -Navalny

Navalny na iya mutuwa a kurkuku muddun ba'a dauki mataki ba - Likitoci

Babban mai sukar gwamnan Rasha Alexei Navalny wanda yanzu haka ke fama da rashin lafiya a kurkukun da ake tsare da shi.
Babban mai sukar gwamnan Rasha Alexei Navalny wanda yanzu haka ke fama da rashin lafiya a kurkukun da ake tsare da shi. Handout Moscow City Court press service/AFP

Likitoci a kasar Rasha sunyi gargadi dangane da tabarbarewar lafiyar babban mai sukan gwamnatin Kremlin Alexei Navalny wanda yanzu haka ke tsare a gidan yari, suna mai cewa zai iya mutuwa a ko wane lokaci, saboda bugun zuciya.

Talla

A ranar 31 ga Maris, babban dan adawar Shugaba Vladimir Putin ya shiga yajin cin abinci don neman kyakkyawan kulawar lafiyarsa saboda matsalolin ciwon baya da kafafuwa da kuma hannayensa.

Jiya Asabar, Shugaban Amurka Joe Biden ya bi sahun wasu shugabannin kasashen duniya da kungiyoyi da ke tir da halin da Navalny yake ciki, yana mai bayyana lamarin da rashin adalci.

A watan Fabrairu aka tura Navalny, mai shekaru 44, kukuru bayan hukuncin shekaru biyu da rabi, bisa laifin almubazzaranci.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.