Faransa

'Yan sanda sun gargadi Macron kan yawaitar tashin hankali a Faransa

Shugaban Faransa Emmanuel Macron.
Shugaban Faransa Emmanuel Macron. Guillaume HORCAJUELO POOL/AFP

‘Yan Sanda a Faransa sun gargadi shugaba Emmanuel Macron akan karuwar tashe tashen hankalun da ake gani a titunan kasar a daidai lokacin da ya ziyarci wasu wuraren da matsalar tafi kamari saboda munin lamarin.

Talla

Tashe tashen hankulan da ake samu a 'yan kwanakin nan sun jefa matukar fargaba a zukatan jama'a, abinda ya zama batun cece kuce a fagen siyasar kasar ganin cewa a shekara mai zuwa za a gudanar da zaben shugaban kasa.

An zagaya da shugaban unguwanni marasa karfi a cikin motar 'yan sanda inda ya ganewa idanun sa inda ake hada hadar kwayoyi.

Batun tsaro ya zama abinda ya mamaye fagen siyasar Faransa yanzu haka.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.