Rasha-Navalny

Likitocin Navalny sun bukaci gaggauta dakatar da yajin abincin da ya ke

Tawagar likitocin Alexei Navalny jagoran adawar Rasha.
Tawagar likitocin Alexei Navalny jagoran adawar Rasha. AP - Kirill Zarubin

Likitocin jagoran adawa na Rasha Alexie Navalny sun bukace shi da ya gaggauta dakatar da yajin cin abincin da ya ke yi bayan kwashe makwanni 3 da farawa abinda ke barazana ga rayuwar sa.

Talla

Likitan na Navalny, Yaroslav Ashikhmin tare da wasu abokan aikin sa 4 sun gabatar da sanarwar da ta ke bukatar Navalny ya kawo karshen matakin da ya dauka domin tsira da rayuwar sa.

Sanarwar da aka wallafa a wata jarida mai zaman kan ta ta Mediazona ta ce muddin aka samu dan lokaci ya na ci gaba da gudanar da yajin za su rasa damar iya kula da shi.

Likitocin sun yaba da goyan bayan da ya ke samu yayinda aka kai shi wani asibitin fararen hula da ke Vladimir domin bai wa wasu likitoci damar duba shi.

A larabar da gabata dubban magoya bayan sa sun gudanar da zanga zanga a birnin Moscow da wasu garuruwa domin bukatar ganin an sake shi.

Kasashen duniya da dama cikin su harda Amurka da Faransa da Jamus da kungiyar kasashen Turai duk sun bukaci gagaguta sakin Navalny wanda ke cikin mawuyacin hali, yayin da Amurka ta yi barazanar daukar mataki mai tsauri kan Rasha muddin dan adawar ya mutu.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.