Rasha-Ukraine

Rasha ta fara janye dakarunta daga iyakarta da Ukraine

Wasu sojojin Rasha yayin fareti a Crimea.
Wasu sojojin Rasha yayin fareti a Crimea. AFP PHOTO/VASILY BATANOV

Kasar Rasha ta fara janye dakarun ta daga kan iyakar Ukraine makkoni biyu bayan da zaman tankiya ke ci gaba da ruruwa a tsakanin Rasha da kasahen Turai a game da yadda kasar ta jibge dakarunta a kan iyakar Ukraine din.

Talla

Kasahen Turai din na ganin cewa jibge dakarun da Rashar ta yi a kan iyakarta, ne ke kara ta’azzara rikicin gabashin Ukraine.

A cewar wasu daga cikin kasashen Turai, jibge dakarun na Rasha a iyakar Ukraine ya taka rawa kwarai wajen kara rura wutar rikicin, abin da ya sanya kasashen ke gargadin Rasha kan abin da kaje ya zo.

Sai dai a yammacin jiya Alhamis, kasar ta Rasha ta tabbatar da cewa tuni ta fara janye dakarunta da yawan su ya kai dubu 10 daga kan iyakar Ukraine din.

A cewar ministan tsaron Rasha Sergei Shoigu, tuni aka yi tsare-tsaren yadda dakarun za su koma gida, yana mai cewa akwai wadanda za’a kwashe ta jirgin kasa, wasu ta jirgin sama yayin da za’a kwashe wasu ta jiragen ruwa.

Tuni kasar Ukraine, ta bakin ministan harkokin wajen ta  Dmytro Kuleba ta yaba da matakin na Rasha, inda ta ce hakan zai saukaka  rikicin da ya taso, duk kuwa da cewa janye dakarun na Rasha kadai ba shi ne zai kawo karshen matsalar baki daya ba.

Wannan ce ta sa kasar ta Ukraine ta kara yin kira ga kawayen ta da su ci gaba da sanya idanu kan yadda al’amurra ke tafiya don kada daga bisani Rashar ta kirkiro da wani sabon abu kuma.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.