Turkiya - Kurdawa

Turkiya ta kaddamar da sobon farmaki kan Ƙurɗawa a Iraki

Shigaban Turkiya Recef Tayyip Erdogan a ranar 9 ga watan Maris  2020
Shigaban Turkiya Recef Tayyip Erdogan a ranar 9 ga watan Maris 2020 REUTERS - YVES HERMAN

Sojojin Turkiyya sun kaddamar da wani sabon farmaki ta kasa da ta sama kan haramtattun sansanonin mayakan Kurdawa a arewacin Iraki.

Talla

Ma'aikatar tsaron Turkiya ta bayyana kasancewar dakarun kasar a Iraki cikin wani sakon Tweeter ba tare da bayyana yawan adadin suba.

Kafofin yada labaran Turkiya sun ce sojojin Ƙasa sun sauka a yankin Metina cikin jirage masu saukar ungulu yayin da jiragen yakin suka jefa bama-bamai a kan wuraren da kungiyar Kurdawa ta (PKK) suke.

Gidan talibijin na Turkiya ya nuna hotunan sojoji dira daga jirage masu saukar ungulu, yayin da sojojin kasa ke harba bindigogi.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.