Faransa-Rasha

Macron ya gargadi Putin kan kula da lafiyar Alexei Navalny

Wata ganawar Shugaba Emmanuel Macron da Vladimir Putin na Rasha.
Wata ganawar Shugaba Emmanuel Macron da Vladimir Putin na Rasha. REUTERS/Philippe Wojazer

Shugaban Faransa Emmanuel Macron ya ce kasar ta matukar damuwa da halin da jagoran adawar Rasha Alexei Navalny ke ciki bayan tsanantar rashin lafiyarsa sakamakon yajin abinci na mako 3 da ya yi don adawa da tsarewar da hukumomin Moscow ke masa.

Talla

Macron wanda ke sanar da hakan yayin wata zantawarsa ta waya da shugaban Rasha Vladimir Putin ya ce akwai bukatar bai wa lafiya jagoran adawar cikakkiyar kulawa don tseratar da rayuwarsa daga barazanar da likitoci suka ce yana fuskanta.

Sanarwar da fadar Elysee ta fitar wadda ke sanar da tattaunawar tsakanin Macron da Putin ta ce shugaban na Faransa ya ja kunnen takwaransa na Rasha don baiwa Navalny cikakkiyar kulawa.

Kasashen yammacin Duniya dai na ci gaba da caccakar Rasha game da tsare jagoran adawar yayinda Amurka ta yi barazanar daukar mataki muddin Navalny ya rasa ransa a hannun mahukuntan kasar.

Tuni dai Rasha ta dauke Navalny daga asibitin gidan yarin zuwa wani asibiti daban don bashi kulawa dai dai lokacin da ya kawo karshen yajin abincin da ya ke bayan shawarwarin likitoci.

A bangare guda Shugaba Vladimir Putin ya sake jan kunnen kasashen yammacin game da yiwa Rasha kutse a harkokinta na cikin gida, yayinda ya yi barazanar daukar mataki matukar tura ta kai bango.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.