Faransa-Tsaro

Firaministan Faransa ya yi tir da wasikar tsoffin Sojin kasar ga gwamnati

Firaministan Faransa Jean Castex lokacin da ya ke jawabi cikin fushi kan wasikar da tsaffin sojin kasar suka aikewa gwamnati.
Firaministan Faransa Jean Castex lokacin da ya ke jawabi cikin fushi kan wasikar da tsaffin sojin kasar suka aikewa gwamnati. AFP - BERTRAND GUAY

Firaministan Faransa Jean Castex ya caccaki wasikar da tsoffin manyan Sojin kasar suka aikewa gwamnati da ke gargadi kan yiwuwar barkewar rikici a kasar, inda ya bayyana wasikar da abin kunya ga bangaren Soji.

Talla

Firaminista Jean Castex wanda ya yi wadai da wasikar ta tsaffin janarorin Sojin, ya ce ko kadan gwamnatin Faransa ba za ta lamunci shigar sojoji harkar siyasa ba, wanda zai iya shafar mutuncin bangaren.

Tuni ministar tsaron Faransar Florence Parly ta yi barazanar gurfanar da tsaffin Sojin bayan kafa kwamitin bincike don gano masu hannu a wasikar wadda Faransa ta yi ikirarin cewa za ta iya haddasa rikici a kasar bayan tsagwaron wariyar da ke tattare cikinta.  

Bayanai sun ce cikin wadanda suka rattaba hannu a wasikar har da Jean-Pierre Fabre-Bernadac tsohon sojan kasar tun 1990 da kuma Janar Antoine Martinez tsohon Soja da ke jagoranci wata kungiyar kare hakkin dan adam a yanzu.

Wasikar wadda ta hada tsaffin Sojin kasar ta Faransa da ma wadanda ke bakin aiki a yanzu da suka mikawa gwamnatin kasar, a cewa gwamnati gargadin da ke cikinta na bukatar afkawa wasu mutane wanda gwamnatin ta kira da kokarin haddasa rikici da kuma tunzura jama’a.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.