Faransa-Coronavirus

Faransa za ta sake bude wuraren shakatawa

Shugaban Faransa Emmanuel Macron.
Shugaban Faransa Emmanuel Macron. CHRISTIAN HARTMANN POOL/AFP/File

Shugaban Faransa Emmanuel Macron ya sanar da aniyar gwamnatinsa ta sake bude gidajen shayi, barasa da na cin abinci da sauran sana’o’i a matakai dabam  -dabam, bayan rufe su da aka yi don dakile annobar  coronavirus.

Talla

A wata sanarwa da al’ummar kasar suka yi ta dako, shugaba Macron ya ce za a sake bude gidajen ajiyar kayayyakin tarihi da silma, da gidajen rawa daga ranar 19 ga watan Mayu, amma gidajen shayi da na cin abinci za su dan dakata har sai ranar 9 ga watan Yuni, sai dai an ba su damar  biyan bukatun abokan hulda a duk inda suke.

Macron  ya kuma bayar da jadawalin  sassauta dokar hana yawon dare da al’ummar biranen kasar suka tsana, wadda ke fara aiki daga karfe 7 na dare,  inda ya ce daga karfe 9 na dare dokar za ta fara aiki daga ranar 19 ga watan Mayu, daga 9 ga watan Yuni kuwa ta fara aiki daga karfe 11 na dare, kafin a dage ta gaba daya a ranar 30 ga Yuni.

Faransa na daf da kawo karshen killace gari karo na 3 da ta sanya a kokarinta na taka wa annobar Covid 19 da ta kunno kai a karo na 3 birki.

A  ranar Alhamis aka samu karin wadanda wannan cuta ta aika lahira a cikin sa’o’i 24 da suka gabaci ranar, abin da  ya kawo jimilar mamata sakamakon anobar dubu dari da 3, da dari 9 da 47.

Adadin masu kamuwa da cutar Korona ya ragu daga dubu 40 zuwa  dubu 27 tun daga cikin watan da ya gabata.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.