Amurka-Afghanistan

Amurka ta fara janye rukunin karshe na dakarunta daga Afghanistan

sakataren harkokin wajen Amurka Antony Blinken.
sakataren harkokin wajen Amurka Antony Blinken. MANDEL NGAN POOL/AFP/File

A Asabar dinnan  Amurka ke janye rukunin karshe na dakarunta daga Afghanistan  a hukumance, lamarin da ke kawo yakin da ta fi dadewa tana yi a tarihinta, amma kuma ta jefa makomar Afghanistan cikin halin rashin tabbas, a daidai lokacin da kungiyar Taliban ke dada samun kwarin gwiwa.

Talla

Jami’an Amurka da ke Afghanistan a halin yanzu sun ce wannan janyewa ta dakarun kasar wata aba ce da aka fara, kuma ci gaba ake a wannan rana ta 1 ga watan Mayu.

Sai karar jirage masu saukar ungulu na Amurka ake ji daga sararin samaniyar Kabul da kuma sansanin sojin sama dake garin Bagram, biyo bayan janyewar dakarun NATO  da aka fara a ranar Alhamis da ta gabata.

Rundunonin tsaron Afghanistan na cikin shirin ko-ta- kwana, don dakile duk wanda zai afka wa dakarun da ake  janyewa.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.