Faransa-Coronavirus

Faransa da gano mutane 3 dauke da sabon nau'in korona ta ya bulla a India

Sashin gobe da nisa na wani asibitin da ake kula da masu tsanin korona a Paris na kasar Faransa
Sashin gobe da nisa na wani asibitin da ake kula da masu tsanin korona a Paris na kasar Faransa © Benoit Tessier/Reuters

Faransa ta gano mutane uku dake dauke da sabon nau’in cutar korona na B.1.617 da yanzu haka ke addabar India a cikin kasar.

Talla

Ministan lafiyar kasar Olivier Veren wanda ya bayyana haka ta shafinsa na Twitta yace yanzu haka an killace mutanen, wanda na ukun ya shigo kasar ne daga India, kuma ana ci gaba da laluben wadanda sukayi mu’amala da su.

Matasa za su fara karbar rigakafin Covid-19 daga watan Yuni

A wani labarin kuma Shugaban na Faransa Emmanuel Macron ya sanar da shirin fara yiwa ilahirin ‘yan kasar  da shekarunsu ya kai 18 zuwa 50 rigakafin Covid-19 nan da watan Yuni mai zuwa, matakin da ke zuwa a dai dai lokacin da kasar ke shirin sassauta dokar kulle.

Emmanuel Macron wanda ke sanar da matakin ta shafinsa na Twitter ya ce daga ranar 15 ga watan Yuni za a bude rijistar allurar ga matasa ‘yan shekaru 18 zuwa 50 yayinda wadanda shekarunsu ya haura 55 kuma su ke cikin wani yanayi ka iya rijistar don karbar allurar.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.