Faransa - Coronavirus

An kama masu bijirewa dokokin korona a Faransa

Wata ma'aikaciyar jinya dake aiki a sashin gobe da nisa na masu dauke da cutar korona a Faransa  28, Oktoban 2020.
Wata ma'aikaciyar jinya dake aiki a sashin gobe da nisa na masu dauke da cutar korona a Faransa 28, Oktoban 2020. AP - Daniel Cole

'Yan sanda da jandarmomi a Faransa sun tarwatsa kimanin mutane 400 da suka halarci wani bikin kida da rawa na sarari da aka shirya ranar Assabar da ta gabata a wani wuri dake  kusa da Dijon dake  tsakkiya maso gabashin kasar, kwana guda bayan gudanar da haramtacen biki a yankin yammacin kasar, duk kuwa da matakin killace jama’a saboda annobar corona da gwamnati  ta dauka.

Talla

Casun kida da wakar na sararin  "free-party" da aka gudanar karkashin wata jibgegiyar rumfa da aka feshe da maganin kashe kwayoyin cuta a wata karamar hukuma dake yankin Couchey, mai tazarar kilo mita sama da 10 da Dijon, ya kawo karshe bayan da jami’an jandarma su ka yi masa dirar mikiya tare da canfake wanda suka shirya shi, kamar yadda mahukumtan yankin saka sanar

Kantoman yankin Bourgogne-Franche-Comté Fabien Sudry ya sanar da AFP yin tir da Allah waddai da faruwar lamarin da ya danganta da rashin sanin ciwon kai a wannan lokaci da ake faman yaki da annobar a kasar, in da ya kara da cewa lokaci bai yi ba da ya kamata a yi saku saku da yaki da ake yi da annobar ta Covid 19.

Kantoman ya kara da cewa Jam’ian tsaro sun tarwatsa haramtacen bikin ne da misalin 8 na daren tare da mamaye yankin da kimanin 'yan sanda da jandarmomi 140 da aka tura suka yi. Bayan haka kuma wani jirgi mai saukar angulun na jandarma ya ci gaba da shawagin sintirin tsaro a yankin.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.