Faransa - Masar

Faransa ta sayar wa Masar jiragen yaki 30 samfurin Rafale

Jiragen yaki samfurin Rafale kan jirgin dako na Charles de Gaulle, ranar 1 ga watan oktoban 2016
Jiragen yaki samfurin Rafale kan jirgin dako na Charles de Gaulle, ranar 1 ga watan oktoban 2016 Eric Feferberg AFP/Archivos

Faransa ta kulla yarjejeniyar sayar wa Masar jiragen yaki samfurin Rafale guda 30 a kan kudi kusan Euro milyan dubu 4.

Talla

A sanarwar da ta fitar a wannan talata, ma’aikatar tsaron Faransa ta bayyana yarjejeniyar a matsayin wadda ke kara tabbatar da kyakkyawar alaka tsakanin kasashen biyu.

Karkashin wannan yarjejeniya, Faransa ce za ta dauki nauyin bai wa dakarun kasar Masar horo kan yadda ake sarrafa wadannan jirage da kuma kula da su a cewar wata majiya ta kusa da ministar tsaron kasar Florence Parly.

Shugaban Faransa Emmanuel Macron da takwaransa na Masar Abdel Fattah al-Sissi a fadar Elysée birnin Paris ranar 7 disamba 2020.
Shugaban Faransa Emmanuel Macron da takwaransa na Masar Abdel Fattah al-Sissi a fadar Elysée birnin Paris ranar 7 disamba 2020. REUTERS - GONZALO FUENTES

Ana zargin Faransa da kin mutunta hakkin dan adam a Masar

Wannan ciniki na zuwa ne a daidai lokacin mahukuntan kasar Masar ke shan caccaka daga kungiyoyin kare hakkin dan adam da ke zargin su da tauye hakkokin bil adama, yayin da wasu ganin cewa a wannan yanayi sam bai kamata Faransa ta sayar wa kasar da irin wadannan jiragen yaki ba.

Wata cibiyar bincike da ke Faransa mai suna Disclose ce ta fara tsegunta cewa an kulla wannan ciniki, kafin daga bisanin ma’aikatar tsaron kasar ta tabbatar da hakan a wannan talata.

To sai dai ko a shekara ta 2015 Masar ta sayi irin wadannan jirage samfurin Rafale guda 24 daga Faransa.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.