Faransa

Faransa ta yi bikin cika shekaru 200 da mutuwar Napoleon

Shugaban Faransa Emmanuel Macron.
Shugaban Faransa Emmanuel Macron. Ian LANGSDON POOL/AFP

An yau Laraba shugaban Faransa  Emmanuel Macron ya kaddamar da bikin cika shekaru 200 da mutuwar tsohon shugaban kasar, kuma jarumin soji, Napoleon Bonaparte, lamarin da ya janyo cece-kuce a game da mutumin da ke da mahimmanci a tarihin kasar.

Talla

A ranar 5 ga watan Mayu ta shekarar 1821 ne mai girma Napoleon Bonaparte ya mutu yana mai shekaru 51, nesa da iyalansa,  a yankin Saint  Helena, wani tsibiri a kudancin tekun Atlantic, inda turwan Birtaniya suka cilla shi gudun hijira bayan galaba da suka samu a kansa.

Bayan shekaru 200, shugaba Emmanuel Macron ya dora furanni a kan makwancinsa a  majami’ar  Dome des Invalides, inda aka kebe don ajiye wadanda suka jajirce ta wajen nuna jarumta don kare martabar Faransa.

Ana ci gaba da tafka muhawwara a duk lokacin da batun Napoleon ya kunno kai tsakannin masu kare shi, a matsayinsa na tsayayyen soja, kuma wanda ya assasa Faransa a turbar zamanancewa, da kuma masu sukarsa da zarginsa da zama ummul’abaisin mutuwar dubban Faransawa da kuma maido da bauta a kasar.

Shugaba Emmanuel Macron ya gudanar da wannan biki ne duk da cewa rabon da wani shugaba yayi haka tun a shekarar 1969 da shugaba George Pompidour ya yi bikin tunawa da Napoleon, bayan da shugabannin da suka gabace shi suka kauce wa haka.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.