Turai - China

Turai zata dauki mataki kan yadda China ke mamaye kasuwannin yankin

Shugabar kungiyar tarayyar Turai Ursula von der Leyyen yayin wani taro a Bruxelles, ranar 23 ga watan Afrilu 2021.
Shugabar kungiyar tarayyar Turai Ursula von der Leyyen yayin wani taro a Bruxelles, ranar 23 ga watan Afrilu 2021. AP - Francois Walschaerts

Kungiyar Tarayyar Turai na kokarin karfafa matakai na shawo kan mamayar kayayakin China a kasuwannin yankin, matakin da ke zuwa a dai-dai lokacin da kasashen duniya ke ganin China a matsayin barazana ga tattalin arzikin su dama kasuwanci.

Talla

Kwamishiniyar kare kasuwannin Turai Margrethe Vestager ce ta bayyana hakan, inda ta ce ya zama wajibi tarayyar Turai ta dauki mataki, la’akari da yadda China ke yunkurin mayar da yankin kasuwar jibge kayayyakin ta.

A cewar ta, duk da cewa China itace abokiyar kasuwancin tarayyar Turan ta biyu mafi girma, idan aka cire kasar Amurka, amma duk da haka ya zama wajibi a dauki matakin da ya dace.

Dole a takawa China Birki

Tarayyar Turan dai na kokarin yin duk mai yiwuwa wajen ganin ta takawa China burki da kuma yadda Jamus ke kokari wajen sabuntawa da kuma inganta alaka tsakanin ta da Chinan.

Ta cikin wani kundin bayani da kamfanin dillacin labaran Faransa AFP ya samu, ya nuna cewa karkashin wannan kokari da tarayyar Turan ke yi, za kuma ta sanya idanu kan kamfanonin da bana tarayyar turai ba, da kuma wadadda ke bukatar shiga yankin dan kafa kamfanoni.

Kundin bayanin ya kara da cewa za kuma a sake duba yadda wasu kamfanoni da basa biyan haraji, saboda wasu dalilai.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.