Turai-Tattalin arziki

Turai na taron inganta rayuwar jama'a don magance matsalar tattalin arziki

Shugabar Majalisar kungiyar EU Ursula von der Leyen da shugaban kungiyar Charles Michel.
Shugabar Majalisar kungiyar EU Ursula von der Leyen da shugaban kungiyar Charles Michel. AFP - STEPHANIE LECOCQ

Shugabannin kasashen EU 27 na tafka muhawara yau juma’a dangane da shirin yaki da talauci da rashin daidaiton jinsi cikin kasashensu, dai dai lokacin da su ke shirin farfadowa daga illar da annobar covid-19 ta yiwa tattalin arzikinsu, ko da ya ke an samu rarrabuwar kai game da matsayin kungiyar kan shirin sake gina tattalin arzikin kasashen.

Talla

Bayan faro muhawarar ta bidiyon intanet a yau juma’a, babban taron inganta rayuwar jama’ar na EU na shirin hada shugabannin kungiyar 27 a birnin Porto na Portugal daga gobe asabar, inda za su ci gaba da tattaunawa kan batutuwan da suka shafi bai wa bukatun al’umma fifiko, ko da ya ke shugabar gwamnatin Jamus Angela Merkel da Firaministan Holland Mark Rutte za su halarci taron ne ta bidiyon intanet saboda matakan yaki da covid-19.

Taron shugabannin Turan kan Inganta rayuwar al’umma zai mayar da hankali kan yadda za a habaka tattalin arzikin yankin musamman ga masu kananan kasuwanci da masana’antu baya ga jaddada manufar samar da daidaito, ko da ya ke tuni wasu suka fara kalubalantarsa yayinda masu tsattsauran ra’ayi ke shirin gudanar da zanga zanga kan taron.

Taron wanda wani bangare nasa ya faro tun daga yau juma’a amma ta bidiyon intanet, ana saran ya samu halartar manyan ‘yan kasuwa da masana tattalin arziki da shugabancin kungiyoyin kwadadgo dana kasuwanci dama na fararen hula baya ga wasu shugabannin yankin ciki har da Emmanuel Macron na Faransa.

Firaministan Portugal Antonia Costa mai masaukin baki ya ce annobar covid-19 ta nuna karara gibin da ake da shi wajen daidaiton jinsi dama yawaitar bukatun al’umma da ke neman kulawar gwamnatoci.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI