Isra'ila-Falasdinu

Sabuwar tarzoma ta raunata da dama a birnin Kudus

'Yan sandan Isra'ila a kokarinsu na dakile masu zanga-zanga a garin Shiekh jarrah.
'Yan sandan Isra'ila a kokarinsu na dakile masu zanga-zanga a garin Shiekh jarrah. REUTERS - AMMAR AWAD

Mutane da dama sun ji rauni a  yayin da ‘yan sandan Isra’ila suka yi amfani da ruwan zafi tare da harsashen roba wajen tarwatsa Falasdinawa masu zanga-zanga  a gabashin Birnin Kudus da Yahudawa suka mamaye, kwana guda bayan wata mummunar arangama a Masallacin Al-Aqsa.

Talla

Sabon rikicin ya tashi ne kwana guda bayan da sama da mutane 200 suka ji rauni a masallaci, lamarin da ya janyo kiraye –kiyaren kawo karshen tashin hankali daga kasashen duniya.

‘Yan sanda sun ce sun tarwatsa wani gungun masu zanga-zanga a yankin Sheikh Jarrah, inda dimbim mutane suka taru, su na jifan jami’an tsaro da duwatsu.

A yau Lahadi hukumomi suka ce an harbo wata roka daga Zirin Gaza, inda dakarun tsaron Isra’ila suka gaggauta mayar da martani.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI