Rasha

Dan bindiga ya kashe yara 'yan makaranta 7 a birnin Kazan na Rasha

Harabar makarantar da harin na birnin Kazan ya faru a Rasha.
Harabar makarantar da harin na birnin Kazan ya faru a Rasha. AP - Roman Kruchinin

Dan bindiga ya kashe mutane akalla 7 mafi akasarinsu yara kanana, a yayin harin da suka kai kan wata makaranta da ke birnin Kazan a kasar Rasha.

Talla

Cikin bayanan farko da suka fitar jami’an tsaron Rasha sun ce mutum guda ne ya kai farmakin, yayinda wasu majiyoyin suka ce ‘yan bindiga ne guda 2, ciki har da wanda jami’an tsaron suka kashe.

Wani hoton bidiyo da ke yawo a kafafen sada zumunta ya nuna yadda mutane suka rika yin kundumbala ta hanyar dako tsalle zuwa kasa daga wundunan benayen da ke hawa biyu da na uku a makarantar da ke birnin na Kazan, a dai dai lokacin da ake jiwo karar harbin bindiga.

An dai samu bayanai masu cin karo da juna kan farmakin na yau, inda cibiyar yaki da ta’addancin kasar Rasha ta ce mutane bakwai suka rasa rayukansu a harin, kuma dukkansu yara ne yayin da wasu 16 suka jikkata.

Sai dai Magajin garin birnin na Kazan ya ce mutane 8 suka mutu, yayin da wasu kafofin yada labarai a kasar ta Rasha suka ce adadin ya kai 11.

Kawo yanzu mutum guda jami’an tsaro suka kame, wanda suka ce shi ne ya kai karin kan makarantar, sabanin wasu rahotannin dake cewa mahara biyu suka yi aika aikar.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI