Faransa

Faransa ta bukaci Sojinta da sukai mata wasika kan barazanr yaki su ajje aiki

Ministar tsaron Faransa Florence Parly.
Ministar tsaron Faransa Florence Parly. AP - Thibault Camus

Babban Hafsan sojin Faransa Janar Francois Lecountre ya bukaci sojojin kasar da suka rubuta budaddiyar wasika ga gwamnati inda suke gargadi dangane da barazanar barkewar yaki a kasar da su aje mukaman su.

Talla

A wasikar da ya rubutawa sojojin dake gargadin, Janar din yace abu mafi dacewa a gare su shine su aje mukaman su su kuma fice daga aikin domin cigaba da bayyana manufofin su.

Janar Lecountre yace a cikin makwanni uku da suka gabata, jami‘an sojin sun sabawa dokokin aikin su, inda yake cewa sojojin da suka rattaba hannu akan wasikar sun jefa bangaren sojin cikin mahawarar siyasa da bata dace ba.

Babban hasan sojin yace kowanne soja na da ‚yancin tunani amma kuma ya zama wajibi ya banbance tsakanin aikin soji da na farar hula.

Wadanda suka sanya hannu akan budadiyar wasikar sun bayyana kan su a matsayin matasan dakarun da suka dandana aikin soji.

Wasikun guda biyu da sojojin suka rubuta ta haifar da mahawara a kasar inda ministan tsaro ta bayyana su a matsayin makarkashiyar siyasa, yayin da take tuna musu hakkin dake kan su.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI