Faransa - Hakkin dan Adam

Macron ya fusata da wasikar gargadi kan barazanar barkewar yakin basasa

Shugaban Faransa Emmanuel Macron.
Shugaban Faransa Emmanuel Macron. Ian Langsdon Pool/AFP/Archivos

Gwamnatin shugaban Faransa Emmanuel Macron  ta maida martani a fusace, bayan da wasu gungun sojoji suka sake wallafa budaddiyar wasika dake gargadin hadarin da kasar ke ciki na yiwuwar barkewa yakin basasa sakamakon yadda shugaban ke bada kai bori ya hau a game da wasu al’amura da suka shafi addinin Musulunci a kasar.

Talla

Wasikar, wacce aka wallafa a shafin yanar gizon wata mujallar kasar ‘Valeurs Actuelles’ da yammacin ranar Lahadi, ta yi daidai da wacce mujallar ta wallafa a watan da ya gabata, sai dai a wannan karon ta bayyana cewa wasu matasan dakarun da yanzu haka ke cikin aikin ne suka rubuta.

Ministan cikin gida Gerald Darmanin, wanda ke na hannun damar Macron, ya zargi wadanda suka sanya hannu a wasikar ta biyu da rashin "kwarin gwiwa kana bin da suka rubuta,  yayin da Ministan Tsaro Florence Parly ta yi watsi da shi a matsayin wani bangare na "makircin siyasa".

To sai dai kuma, tuni matar da ake kallon a matsayin babbar abokiyar hamayyar Macron da za ta fafata da shugaban a badi, Marie Le Pen tayi maraba da wasikar.

Jagorar 'yan adawa a Faransa Marine Le Pen ta jam'iyyar Front National.
Jagorar 'yan adawa a Faransa Marine Le Pen ta jam'iyyar Front National. AFP - LIONEL BONAVENTURE

Wasu daga cikin gwamnatin sun zargi Le Pen, tun bayan da aka wallafa wasikar farko, wacce ta samu sanya hannun wasu tsirarun jami’ai da kuma kusan Janar-Janar 20 dake daf da ritaya.

Tuni gwamnatin ta sha alwashin hukunta sojojin, saboda a cewar ta babu abinda ke kunshe cikin wasikar face tsantsar nuna wariya, da kalaman tunzuri.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI