Faransa-Yanayi

Macron zai sanya batun sauyin yanayi a kundin tsarin mulkin Faransa

Shyagaban Faransa Emmanuel Macron.
Shyagaban Faransa Emmanuel Macron. REUTERS - POOL

Shugaba Emmanuel Macron na Faransa, ya lashi takobi sanya batun sauyin yanayi a cikin kundin tsarin mulkin kasar ta hanyar shirya kuri’ar jin ra’ayin jama’a, bayan da ya gaza samun goyon bayan Majalisar dattawan kasar kan wannan batu.

Talla

Batun kare muhalli da kuma yaki da dumamar yanayi, abubuwa ne da sbugaba Macron ya yi alkawari tabbatar da su cikin kundin tsarin mulkin kasar tun cikin shekarar da ta gabata, to amma hakan ba zai yiyu ba sai tare da amincewar majalisun dokokin kasar.

Tun da farko dai Macron ya ce ko da amincewar majalisun ko kuma a’a, ba makawa zai gabatar da shi gaban ‘yan kasa domin samun amincewarsu tare da tabbatar da shi a cikin kundin tsarin mulki, yayin da ya rage shekara daya a gudanar da zaben shugabancin kasar.

A cikin zauren majalisar wakilan kasar inda Macron ke da rinjaye, nan take wannan kuduri ya samu amincewar ‘yan majalisar, to sai dai lokacin da aka gabatar da shi gaban majalisar dattawa inda ‘yan adawa ke da rinjaye, sai aka yi watsi da shi.

Ko a ranar lahadin da ta gabata, dubun dubatar mutane ne suka gudanar da zanga-zanga a sassan kasar ta Faransa, inda suke jaddada bukatar ganin gwamnatin kasar ta yi da gaske wajen tunkarar matsalar sauyin yanayi.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI