Faransa - Brazil

Za'a hukunta Air France da Airbus saboda hadarin da ya kashe mutane 228

Jirgin saman kamfanin Air France kirar Airbus A330 da yayi hadari a shkarar 2009 kuma ya hallaka daukacin mutanen da ke ciki bayan tasowa daga Brazil.
Jirgin saman kamfanin Air France kirar Airbus A330 da yayi hadari a shkarar 2009 kuma ya hallaka daukacin mutanen da ke ciki bayan tasowa daga Brazil. . BRAZILIAN NAVY/AFP/Archivos

Kamfanonin Air France da Airbus zasu amsa tambayoyi dangane da hadarin da jirgin Air France ya yi a shekarar 2009, wanda ya yi sanadiyar kashe mutane 228 a kasar Brazil.

Talla

Matakin kotun daukaka kara dake birnin Paris ya sauya shawarar da aka yanke a shekarar 2019 na kin gurfanar da kowane daga cikin kamfanonin biyu, wato Airbus da ya kera jirgin da kuma Air France dake tafiyar da sufurinsa kan hatsarin jirgin da ya kubcewa matukansa sakamakon dusar kankara.

Iyalan wadanda abin ya shafa sun yi maraba da hukuncin, to sai dai kamfanonin biyu sun ce za su nemi yin watsi da shi a kotu mafi girma na Faransa.

Babu adalci a hukuncin

Airbus ya ce "Hukuncin kotun da aka sanar Laraban nan baiyi amfani da sakamakon binciken hadarin ba.

Yayin da kakakin kamfanin Air France – KLM ya ce, basu da alhakin kan mummunan hatsarin da yayi sanadiyar mutuwar mutane 228.

Reo de Janeiro jirgin ya taso zuwa Paris

A ranar 1 ga watan Yunin shekarar 2009 ne jirgin saman Air France mai lamba AF447 yayi hadari a tekun Atlantic bayan tasowa daga Rio de Janeiro zuwa Paris wanda ya kashe daukacin wadanda ke cikin jirgin.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI