Covid-19: Italiya ta jingine kebe masu shiga kasar daga Turai, Amurka, Isra'ila
Wallafawa ranar:
Kasar Italiya a yau Juma’a ta jingine kebewa da binciken kwakwaf da ake yi wa ‘yan kasashen Kungiyar Turai, da Birtaniya da Isra'ila don gano masu dauke da kwayar cutar coronavirus.
Karkashin sabbin dokokin hana yaduwar cutar corona da ake sa ran a fara aiwatarwa Lahadi mai zuwa, Italiya za ta bar jiragen sama da aka tantance babu mai dauke da kwayar cutar corona daga kasashen Amurka, Canada, Japan da Daular Larabawa zuwa Italy ba tare da wani tsangwama ba.
Kazalika za’a daina hana mutane daga kasar Brazil shiga Italiya.
Ministan lafiya na Italiya Roberto Speranza ya sanya hannu cikin doka da ke amince wa mutane daga kasashen kungiyar Turai, da Birtaniya da Israilla, masu dauke da katin an yi masu alluran rigakafin cutar, ba za’a rika tursasa musu kebe kansu ba na wani lokaci don gano ko suna dauke da cutar corona.
A cewar PM Italiya Mario Draghi maido da harkan tarbar masu yawon shakatawa na da muhimmancin gaske ga tattalin arzikin kasar, kasancewar tana daya daga cikin kasashen Turai da cutar corona ta yi wa barna sosai.
Annobar corona dai ta ragu ainun a kasar ta Italiya dan tsakanin nan, kuma kasar ta sami alluran rigakafin cutar miliyan 26 da ake yi wa mutan kasar miliyan 60
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu