Faransa - Zanga-zanga

Zanga-zangar kin jinin Isra'ila ta koma tarzoma a birnin Paris

Masu zanga-zangar adawa da kasar Isra'ila a birnin Paris.
Masu zanga-zangar adawa da kasar Isra'ila a birnin Paris. AP - Rafael Yaghbozadeh

'Yan sanda a birnin Paris sun yi amfani da feshin ruwa da kuma barkonon tsohuwa wajen tarwatsa daruruwan masu zanga-zangar Allah-wadai da hare-haren Isra’ila kan Falasdinawa a birnin Gaza.

Talla

Tun a makon jiye ne dai rundunar ‘yan sandan Faransa ta haramta gudanar da zanga-zangar, zalika kotu ta tabbatar da haramcin, domin gudun barkewar irin tashin hankalin da aka gani yayin makamanciyar ta da ta gudana yayin yakin da aka gwabza tsakanin Isra’ila da Falasdinawa a shekarar 2014.

Zanga-zangar kin jinin Isra'ila a birnin Paris.
Zanga-zangar kin jinin Isra'ila a birnin Paris. AP - Rafael Yaghbozadeh

A waccan lokacin dai masu zanga-zangar sun yi amfani da damar wajen afkawa mujami’un Yahudawa da wasu muradunsu a sassan kasar ta Faransa.

‘Yan adawa a Faransar dai sun caccaki matakin haramta gudanar da zanga zangar a bana, abinda suka bayyana a matssayin take yancin fadin albarkcin baki.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI