Fafaroma Francis-Myanmar

Fafaroma Francis ya jaddada kiran zaman lafiya a Myanmar

Fafaroma  Francis ya bukaci a zauna lafiya a Myanmar.
Fafaroma Francis ya bukaci a zauna lafiya a Myanmar. REMO CASILLI POOL/AFP

Fafaroma Francis ya gudanar da sujada ta musamman don tunawa kasar Myanmar a Lahadin nan, inda ya jaddada kiraye-kirayen da yake na kawo karshen tashin hankali a kasar da ake ta zub da jini tun bayan juyin mulkin da sojoji suka yi.

Talla

Sujadar Mass  din da aka gudanar a majami’ar Saint Peter Basilica ta birnin Vatican  na  zuwa ne bayan kiraye kirayen zaman lafiya da shi Fafaroma Francis, wanda ya ziyarci Myanmar a watan Nuwamban 2017 ya shafe watanni yana yi.

Wata limamiyar ‘yar asaklin Myanmar  ce ta gabatar da karatun farko cikin harshen Burma a sujadar da ta samu  halartar limamai mata da maza kimanin 200.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.