EU-Belarus

EU na shirin sanya wa Belarus takunkumi

Shugaban Belarus Alexander Lukashenko
Shugaban Belarus Alexander Lukashenko REUTERS - POOL New

Kungiyar Tarayyar Turai ta kira Jakadan Belarus domin nuna bacin ranta kan matakin da gwamnatin kasarsa ta dauka na tilasta wa wani jirgin saman fasinja saukar fuji’a domin cafke wani dan jarida mai sukar lamirin gwamnatin Alexander Lukashenko, yayin da ake sa ran kungiyar ta kakaba wa kasar takunkumai.

Talla

Kungiyar EU ta bayyana wa jakadan Belarus Aleksandr Mikhnevich cewa, sam ba ta ji dadin abin da hukumomin kasar suka yi ba, tana mai cewa hakan ya jefa rayukan fasinjoji cikin hadari.

Sanarwar  da  EU ta fitar ta ce,  kasashen kungiyar ta Tarayyar Turai da wasu cibiyoyin nahiyar  sun yi tur da matakin tilasta wa jirgin saman saukar gaggawa domin kame Roman Protasevich.

Sanarwar ta kara da cewa, wannan matakin na a matsayin yunkuri na baya-bayan nan da gwamnatin Belarus ta dauka  da zummar rufe bakin ‘yan adawar kasar.

EU din ta kuma bukaci Belarus da ta gaggauta sakin dan jaridar.

Nan kusa ake sa ran shugabannin kasashen na Turai su kara fitar da wata  sabuwar sanarwa bayan kammala taronsu da ke gudana a yau a birnin Brussels, kuma ana ganin da yiwuwar su kakaba wa Balarus takunkumai saboda tilata wa jirgin fasinjan na Ryanair saukar fuji’a a birnin Minsk a jiya. Lahadi.  

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.