Belarus - Faransa

Faransa ta hana jirgin saman Belarus ratsa sararin samaniyar ta

Jirgin saman kamfanin Belavia a sararin samaniya yayin shirin sauka a filin jiragen sama na birnin Minsk.
Jirgin saman kamfanin Belavia a sararin samaniya yayin shirin sauka a filin jiragen sama na birnin Minsk. REUTERS - Gleb Garanich

Belarus ta zargi Faransa da aikata fashin sararin samaniya, bayan da hukumomin kasar ta Faransa suka hana wani jirgin saman fasinjan Belarus ratsa sararin samaniyarsu, ta hanyar maida shi birnin Minks, inda ya taso da zummar zuwa Barcelona.

Talla

Kamfanin jiragen sama na Belavia mallakin Belarus ya ce Faransa ta hana jirginsa mai kirar B2869 dauke da fasinjoji 56 ratsa sararin samaniyar ta, zalika sai dai ya shafe kusan sa’o’i a cikin iska kafin ya samu komawa filin jiragen sama na Minsk babban birnin kasar Belarus daga inda ya taso.

Cikin sanarwar da ya fitar a jiya, kakakin ma’aikatar harkokin wajen Belarus Anatoly Glaz, ya yi amfani da kakkausan harshe wajen caccakar Faransa inda ya bayyana katse Balaguron jirginsu da suka yi a matsayin fashin sararin samaniya, bisa umarnin fira ministan kasar ta Faransa.

Kakakin ma’aikatar harkokin wajen na Belarus ya ce mafi akasarin fasinjojin dake jirgin saman da Faransa ta haramtawa ratsa samanta ‘yab kasashen kungiyar tarayyar turai ne EU, wadanda aka jefa rayuwarsu cikin hatsari.

Jirgin saman kamfanin Ryanair da gwamnatin kasar Belarus ta karkatar da akalarsa ta hanyar tilasta masa sauka a filin jiragen sama na Minsk. 23/05/2021.
Jirgin saman kamfanin Ryanair da gwamnatin kasar Belarus ta karkatar da akalarsa ta hanyar tilasta masa sauka a filin jiragen sama na Minsk. 23/05/2021. REUTERS - ANDRIUS SYTAS

Ranar Lahadi hukumomin Belarus suka karkatar da akalar wani jirgin fasinjan kamfanin Ryanair, inda suka tilasta masa sauka a filin jiragen saman birnin Minsk domin kama Roman Protasevich wani mai fafutuka da yayi kaurin suna wajen adawa da shugaban kasar ta Belarus Alexander Lukashenko.

Tun a karshen makon ne dai matakin na Belarus ya janyowa shugaba Lukashenko kakkausar suka daga kasashen Turai, abinda ya sanya kungiyar EU haramtawa dukkanin jiragen saman kasar Belarus din shawagi a sararin samaniyar ilahirin kasashen da suke karkashinta.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI