Faransa-Coronavirus

Faransa za ta fara yi wa yara allurar Korona

Shugaban Faransa  Emmanuel Macron.
Shugaban Faransa Emmanuel Macron. AFP - BERTRAND GUAY

Shugaban Faransa Emmanuel Macron ya sanar da cewar daga ranar 15 ga wannan wata kasar za ta fara bai wa yara masu shekaru tsakanin 12 zuwa 18 allurar rigakafin cutar korona.

Talla

Yayin ran-gadin da ya kaddamar na kasa baki daya, shugaba Macron da ke shirin tsayawa takarar zaben shekara mai zuwa, ya shaida wa mutanen kauyen Saint-Cirq-Lapopie da ke kudancin Faransa cewar za a fara gabatar da allurar ga matasa masu shekaru 12 zuwa 18 bayan ganin kashi 50 na manyan mutanen kasar sun karbi allurar.

Yanke hukuncin yi wa matasa allurar rigakafin na zuwa ne sakamakon mahawarar da kasashen duniya ke ci gaba da yi kan muhimmancin haka ko kuma mayar da hankali kan masu yawan shekaru da cutar korona ta fi yi wa illa.

Shugaba Macron ya bukaci jama’ar kasar da su ci gaba da sanya ido suna daukar matakan kariya da amfani da kyallen rufe baki da hanci duk lokacin da suka bar gidajensu.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.