Birtaniya-Corona

Karon farko Birtaniya ta wayi gari babu rahoton mutuwa sanadin corona

Wannan ce rana ta farko tun bayan watan Yulin bara da Birtaniyar ke wayar gari ba tare da rahoton wanda corona ta kashe ba.
Wannan ce rana ta farko tun bayan watan Yulin bara da Birtaniyar ke wayar gari ba tare da rahoton wanda corona ta kashe ba. AP - Markus Schreiber

A karon farko tun daga watan Yulin bara an wayi gari ba tare da samun wanda ya mutu sanaiyyar cutar corona a Birtaniya ba, annobar cutar da zuwa yanzu ta halaka mutane dubu 127 da 782 tun bayan bullarta a kasar cikin shekarar 2020.

Talla

Rashin wadanda suka mutu sakamakon cutar jiya Talata na zuwa ne kwana guda bayan gwamnati ta ce mutuum guda ne ya mutu sakamakon cutar a ranar litinin.

Sakataren lafiya Matt Hancock ya bayyana farin cikin sa da matakin, wanda ya bayyana a matsayin gagarumar ci gaba sakamakon matakan rigakafin da suka kaddamar.

Kafin yanzu dai Birtaniya ta zama sahun gaba a jerin kasashen Turai da cutar ta fi yiwa barna duk da matakan kariya da ta rika dauka, yayinda bullar sabuwar nau'in cutar ta corona mai matukar karfi ya tilasta sake tsaurara dokoki a sassan kasar da kuma ci gaba da killace baki masu shiga daga sassan Duniya.

Tuni dai kasar ta sassauta dokokin takaita walwalar jama'a da ta sanyawa al'ummarta ko da ya ke har yanzu akwai dokokin killace kai ga duk wani baki da ya shiga kasar daga wasu kebantattun kasashe.

Haka Zalika Birtaniya na matsayin 'yan sahun gaba da ke yiwa al'ummarsu rigakafin cutar ta corona da nufin gaggauta dawo da rayuwa gabanin bullar corona.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.