Faransa-Armenia

Macron ya bukaci gaggauta ficewar dakarun Azerbaijan daga Armenia

Shugaban Faransa Emmanuel Macron yayin karbar bakoncin Firaministan rikon kwarya na Armenia Nikol Pashinyan.
Shugaban Faransa Emmanuel Macron yayin karbar bakoncin Firaministan rikon kwarya na Armenia Nikol Pashinyan. AP - Francois Mori

Shugaba Emmanuel Macron na Faransa ya bukaci gaggauta ficewar dakarun Azerbaijan daga Armenia bayan tashe-tashen hankulan da aka samu cikin makon jiya da ya sanya fargabar yiwuwar dawowar rikici tsakanin bangarorin biyu.

Talla

Macron wanda ke karbar bakoncin Firaministan rikon kwarya na Armenia Nikol Pashinyan a birnin Paris, y ace har yanzu akwai muhimman matakai da ya kamata a dauka don kaucewa sake fuskantar rikicin da bangarorin biyu suka yi a baya-bayan nan.

A bara ne kasashen na Armenia da Azerbaijan suka tafka yakin makwanni 6 wanda ya lakume rayukan dakarun bangarorin biyu makwabtan juna, rikici mafi muni da suka gani cikin kusan shekaru 20, gabanin cimma kwarya kwarya yarjejeniyar zaman lafiya da ta dakatar da yakin.

Sai dai Emmanuel Macron wanda ke matsayin aboki ga kasar ta Armenia, ya ce ficewar dakarun na Azerbaijan ne zai tabbatar da wanzuwar yarjejeniyar tsagaita wuta da bangarorin biyu suka cimma cikin 2020.

Faransa da Turkiya wadanda dukkaninsu mambobin kungiyar tsaro ta NATO ne kowaccensu na goyon bayan kasa guda a yakin wanda Azerbaijan ta yi nasara kan Armenia dangane da yankin da s uke takaddama kanshi tsawon shekaru.

A cewar Emmanuel Macron bangarorin biyu ka iya cimma daidaito kan wanzajjen zaman lafiya ba tare da barazanar Soji ko kuma girke dakarun wani bangaren a wani bangare ba.

Ziyarar Firaministan rikon na Armenia na da nufin sake neman cikakken goyon bayan faransa ga yankin.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.