Rasha-siyasa

Sabuwar dokar Rasha za ta hana 'yan adawa takara

Shugaban Rasha Vladimir Putin
Shugaban Rasha Vladimir Putin AP - Sergei Ilyin

Shugaban Rasha Vladimir Putin ya rattaba hannu kan wata sabuwar doka wadda za a fake da ita wajen haramta wa ‘yan adawa tsayawa takara a zabukan kasar.

Talla

Ana sa ran wannan doka za ta hana mukarraban jagoran ‘yan adawar Rasha Alexei Navalny fafatawa a zaben kasar.

Ita dai gwamnatin kasar cewa ta yi, dokar za ta haramta wa kungiyoyin  masu tsattsauran ra’ayi tsayawa takara a zaben majalisar dokokin kasar.

Sai dai tuni manazarta suka fara sukar dokar, suna masu kallon ta a matsayin wani yunkuri na baya-bayan nan domin murkushe ‘yan adawa gabanin zaben da za a gudanar a cikin watan Satumba mai zuwa.

A cikin  makon nan ne wannan doka ta samu amincewar ‘yan majalisar dattawar kasar da gagarumin rinjaye.

Wannan na zuwa ne a yayin da wata kotun Rasha ke nazarin ayyana cibiyar siyasar Navalny a matsayin ta masu tsattsauran ra’a’ayi, kuma ana dakon hukuncin kotun nan da farkon makon gobe.

Matakin na shugaba Putin zai shafi hatta dubban Rashawan da ke bada tallafi ga cibiyar siyasar ta Navalny.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.