Faransa-Macron

Shugaban Faransa ya kauce wa bada tabbacin sake tsayawa takara

Shugaban Faransa Emmanuel Macron.
Shugaban Faransa Emmanuel Macron. Bertrand Guay AFP

Shugaban Faransa Emmanuel Macron ya ce yana shirin daukar matakai masu matukar sarkakiya a wannan bazarar, inda a wannan karon ma ya kauce bada tabbacin cewa zai sake tsayawa takarar shugabancin kasar don neman wani wa’adin shekaru biyar a zabe mai zuwa.

Talla

Macron ya shaida wa wasu rukunin masu karbar fansho a kauyen Martel dake kudancin Faransa, a wani rangadin da yake a fadin kasar cewa ba zai dauki al’amura  da sauki ba a wannan bazarar.

Da aka tambaye shi ko zai sake neman darewa karagar mulkin kasar a zabe mai zuwa, shugaban mai sassaucin ra’ayi, wanda nasararsa a zaben shekarar 2017 ta sauya alkiblar siyasar kasar ya ce kawo amsar tambayar tamkar riga malam masallaci ne.

Shugaba Macron ya sha yin kaffa kaffa da batun zaben shekarar 2022, duk da cewa  abokan hamayyarsa irin su jagoran masu tsatsauran ra’ayi Marine Le Pen da kusa a bangaren masu ra’ayin mazan jiya Xavier Bertrand tuni suka sanar da aniyarsu ta takarar shugabancin kasar ta Faransa.

Shugaba         Macron, wanda tsohon ma’aikacin banki ne ya dare karagar shugabancin kasar ne da alkwarin tayar da komadar tattalin arzikin kasar, amma wasu manufofinsa sun janyo caccaka, har da zanga-zangar Yello Vest, inda masu gudanar da ita ke zarginsa da fifita ‘yan birni masu hannu da shuni.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.