Belarus

Dan jaridar Belarus dake tsare ya jinjinawa Lukashenko cikin wani hoton bidiyo

Dan jaridar Belarus kuma dan adawa Roman Protassevitch yayin da ya bayyana a wani hoton bidiyo 25 ga watan Mayu 2021
Dan jaridar Belarus kuma dan adawa Roman Protassevitch yayin da ya bayyana a wani hoton bidiyo 25 ga watan Mayu 2021 © Twitter

Dan jaridar Belarus din nan Roman Protasevich, wanda aka tsare bayan an tilastawa jirgin da yake ciki sauka a Minsk, ya bayyana karon farko a gidan talabijin din kasar ranar Alhamis a wata hira mai cike da hawaye wanda dangi da masu fafutukan neman sakinsa suka ce an tilas ta masa ne.

Talla

Da yake ba jawabi cikin bidiyon a wani yanayin rashin walwala, Protasevich wanda ya mallaki wani shafin Telegram na ‘yan adawa Nexta, wanda ya tallata zanga-zangar adawa da gwamnati - ya yi ikirarin shirya zanga-zangar ta bara tare da kalaman yaba wa shugaban kasar Belarus Alexander Lukashenko.

A ƙarshen tattaunawar na awa 1.5 da gidan telebijin na Belarus ya watsa ranar Alhamis da yamma, Protasevich ya rufe fuskarsa da hannuwansa, bayan da ya fara zubda hawaye.

An tilasta masa hirar

Mahaifin dan jaridar mai shekaru 26, Dmitry Protasevich, ya ce anyi bidiyon ne ta hanyar "cin zarafi da azabtarwa da kuma barazana."

"Na san dana sosai kuma na yi imanin cewa ba zai taba fadin irin wadannan maganganun ba,"

kamar yadda ya shaidawa AFP.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI