Faransa - Coronavirus

Faransa zata fara karban masu yawon bude ido daga kasashen duniya

Filin tashi da saukar jiragen saman Faransa na Roissy Charles-de-Gaulle, 1 ga watan Fabarairu 2021.
Filin tashi da saukar jiragen saman Faransa na Roissy Charles-de-Gaulle, 1 ga watan Fabarairu 2021. © AFP - Christophe Archambault

Ya zuwa ranar 9 ga watan Yuni, Faransa za ta sake buɗe iyakokinta ga masu yawon buɗe ido daga kasashe duniya.

Talla

Matakin da zai cire buƙatar nuna gwajin coronavirus ga masu fitowa daga yankin Turai da suka karbi rigakafin korona,  da kuma baiwa masu yawon bude daga sassan duniya izinin shiga kasar muddun sun karbi allurar rigakafin, ciki harda Amurkawa amma sai sun nuna shaidar dake tabbatar da basa dauke da cutar.

Sabbin dokokin da aka sassauta za su bunkasa bangaren yawon bude ido na Faransa, amma masu yawon bude ido daga kasashen da ke fama da karuwar cutar da kuma sabbin nau’in za su bukaci wani dalili mai gamsarwa game da ziyarar tasu, kuma kasashe 16 lamarin zai shafa, ciki harda Indiya da Afirka ta Kudu da kuma Brazil.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.