Faransa - Birtaniya

Faransa ta yi bukin tunawa da sojojin Birtaniya da suka mutu a yakin duniya na 2

Faransa na bukin Tunawa da sojojin Birtaniya da aka kashe yayin yakin duniya na 2, 6 ga watan Yuni 2021
Faransa na bukin Tunawa da sojojin Birtaniya da aka kashe yayin yakin duniya na 2, 6 ga watan Yuni 2021 Joël SAGET AFP/File

A karon farko ana gudanar da bukin tunawa da ‘yan mazan jiya  da sukayi wa Birtaniya hidima aka kashe a lokacin yakin duniya na biyu, da wasu yaƙe-yaƙe yau Lahadi a arewacin Faransa.

Talla

Bikin Tunawar ta Normandy ya kunshi dakarun Birtaniya kimanin dubu 22 442 maza da mata da suka sadaukar da rayukansu yayin mamayar da Nazi tayiwa Faransa a shekarar 1944, a tsaunukan ƙauyen Normandy na Ver-sur-Mer.

Annobar korona ta hana tsoffin sojojin Burtaniya halartan bukin a Faransa, to amma wasu ‘yan mazan jiya kimanin 100 sun hallara gaban wani makeken akwatin talabijin  a dandalin tunawa da su dake Stafford-shire a  Burtaniya.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.