Amurka-Trump

Trump ya yi jawabi a karon farko tun bayan shan kaye a zaben shugaban Amurka

Tsohon shugaban Amurka, Donald Trump.
Tsohon shugaban Amurka, Donald Trump. Mandel NGAN AFP/Archivos

Tsohon shugaban Amurka Donald Trump ya sake fitowa bainar jama’a a jawabinsa na farko tun da ya sha kaye a zaben kasar da ya gabata a jiya Asabar.

Talla

Tsohon shugaban ya bayyana zaben tsakiyar wa’adi da za  a gudanar a  kasar a shekara mai zuwa  a matsayin ‘gwagwarmayar ceto Amurka’, inda ya bar magoya bayansa cikin wasi wasiwasi a game da shirinsa na  zaben shekarar 2024.

Trump ya samu jinjina ta waje tafi daga magoya bayansa na jam’iyyar Republican, bayan da ya ce a kan idonsu ake salwanta Amurka tun bayan da sha kaye a zaben 2021, inda ya caccaki abokin hamayyarsa da ya kada shi, wato shugaba mai ci, Joe Biden.

Ya bayyana 2024, wato shekarar da za a gudanar da zaben shugaban kasa mai zuwa a matsayin shekarar da yake dako, lamarin da ya janyo mai tafi daga masu sauraron sa a garin Greenville, a arewacin Carolina.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.