Faransa-Macron

Wani ya shararawa shugaban Faransa Emmanuel Macron mari a fuska

Shugaba Emmanuel Macron a Saint-Cirq-Lapopie yayin rangadin da ya ke ci gaba da yi sassan kasar.
Shugaba Emmanuel Macron a Saint-Cirq-Lapopie yayin rangadin da ya ke ci gaba da yi sassan kasar. AFP - LIONEL BONAVENTURE

Wani mutum a Faransa ya mari shugaban kasa Emmanuel Macron a fuska lokacin da ya ke ziyara yankin a kudu maso gabashin kasar a ci gaba da rangadin kasa baki daya da ya fara.

Talla

Bidiyon marin da aka sanya a kafofin sada zumunta da kuma tashar talabijin na BFM ya nuna yadda shugaban ya je domin gaisawa da mutanen a gaban wani shinge, inda mutumin ya mika hannu ya mari shugaban a fuska kafin masu tsaron shugaban su dauke shi, yayin da suka kama mutane biyu nan take.

Shugaban Yankin ya sanar da kama mutumin da ya mari shugaban da kuma wani daban, kuma yanzu haka suna can suna amsa tambayoyi.

Abinda ya faru a kauyen Tain-I’Hermitage a yankin Drome ya nuna tabarbarewar tsaro da kuma mamaye shirin shugaban kasar na ziyarar yankunan kasar domin jin abinda ke faruwa a wurin talakawa.

Ana saran shugaba Macron ya ziyarci yankunan kasar da dama a cikin watanni 2 masu zuwa domin ganawa da masu zabe gaba da gaba bayan kwashe sama da shekara guda ana fama da annobar korona.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.