FBI-Europol

Amfani da fasahar kutse ta taimaka wajen kama batagari 800 a Turai

Yin amfani da fasahar datsar bayanan ya taimake wajen kame tarin masu laifi a Turai.
Yin amfani da fasahar datsar bayanan ya taimake wajen kame tarin masu laifi a Turai. ISSOUF SANOGO AFP/File

Jami’an ‘yan sanda sun yi nasarar kame batagari akalla 800 a sassan Duniya, ta hanyar amfani da wata fasahar nadar bayanai ta boyayyun lambobin wayoyin sadarwa, tsarin da hukumar FBI ta yi amfani da shi tare da wasu hukumomin tsaro na kasa da kasa da ya kai ga samun nasarar wannan kamen.

Talla

Tun farko hukumar FBI ta dasa fasahar ta bin diddigi ga wayoyin sadarwar wanda ya bata damar yin kutse ga wayoyin sadarwar bata garin bayan wadanda ke da gungu mutane 800 a sassa daban daban na Duniya.

Jami’an ‘yan sanda a kasashe 16 suka gudanar da sumame kan maboyar batagarin bayan samun damar karanta bayanan hada-hadarsu ciki har da kiran waya da sauran sakonni, wanda ya bayar da damar kame masu hannu a badakalar makamai da miyagun kwayoyi da kuma kungiyoyin tsageru masu kitsa manyan laifuka.

Amfani da fasahar ta nadar bayanan wayoyin wadanda ake zargi da aikata manyan laifuka ba sabon abu ba ne musamman a kasashen Asiya, wanda ke taimakawa wajen kame tarin masu laifi.

Bayanai sun ce Kasashen Sweden da Finland kadai sun kame batagarin 250 yayinda Australia a bangare guda ta kame wasu 200.

Shirin wanda ya gudana bisa hadakar hukumar FBI da sashen bincike na Australia ta yadda aka rabar ko kuma shigar da tarin wayoyin masu dauke da lambobin kutse tare da bazasu a yankunan wadanda ake zargi, wanda ya bayar da damar nadar duk wasu zantattakin mutanen cikin sauki.

Tuni dai rundunar ‘yan sandan Turai ta yi maraba tare da jinjina aikin bisa jagorancin FBI wanda ta ce ya taimaka wajen dakile wasu kashe-kashe da batagarin suka shirya gudanarwa.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI