Faransa-Macron

Mari bai hana Macron ran-gadinsa ba a Faransa

Shugaban Faransa Emmanuel Macron tare da 'yan jarida bayan aukuwar sharara masa mari
Shugaban Faransa Emmanuel Macron tare da 'yan jarida bayan aukuwar sharara masa mari AP - Philippe Desmazes

Daukacin  bangarorin siyasa na Faransa sun yi tir da marin da wani mutum ya dalla wa shugaban kasar Emmanuel Macron lokacin da yake ziyara a garin Tain-l'Hermitage da ke kudu maso gabashin kasar, yayin da shugaban ya ce, zai ci gaba da ran-gadin da ya kaddamar a wasu yankunan kasar duk da abin da ya faru da shi.

Talla

A yayin ziyarar ta Macron a ranar Talata, shugaban  ya keta jami’an da ke kula da tsaronsa, inda ya isa wurin da aka kebe wa  magoya bayansa da 'yan kallo.

Sai dai da isa wurin, shugaban ya nemi yin musafaha da magoya bayan nasa, inda kuma daya daga cikinsu ya daga hannu ya sharara masa mari.

A yayin aukuwar lamarin, an ji wata murya na cewa, Montjoie Saint Denis, ma'ana, 'ba ma ra’ayin Macron'.

'Yan lokuta da aukuwar wannan lamari, gwamnati ta kaddamar da bincike, yayin da masu tsaron shugaban kasar suka kama mutumin da ya wanke shugaban da mari.

'Yan siyasar Faransa sun yi Allah-wadai da wannan dabiya ta kai wa jami’in gwamnati hari, wanda ba shi ne karon farko ba.

Shugaba Macron ya bayyana cewa, wannan ba zai hana shi ci gaba da aiwatar da manufofin da ya saka a gaba ba.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI