Faransa-Macron

Mutumin da ya mari Macron zai sha daurin watanni 4 a kurkuku

Yadda wani matashi ya gaurawa shugaban Faransa Emmanuel Macron mari a bainar jama'a.
Yadda wani matashi ya gaurawa shugaban Faransa Emmanuel Macron mari a bainar jama'a. © captura de tela

Kotu a Faransa ta zartas da hukuncin daurin watanni 18 kan mutumin da ya shararawa shugaban kasar Emmanuel Macron Mari a Talatar da ta gabata.

Talla

Yayin sanar da hukuncin Kotun ta ce matashin zai yi zaman gidan Yari na tsawon watanni 4 ne a yayin da zai karasa ragowar 14 a karakshin daurin talala.

Yau Alhamis ne dai aka saurari wannan Shari’a inda masu gabatar da kara a kasar ta Faransa suka nemi kotu ta yanke hukuncin na daurin watanni 18 kan Damien Tarel da ya gaurawa shugaba Macron mari a jihar Valence dake kudancin kasar Faransa, in da ya kai ziyarar aiki a wannan makon.

Karkashin dokokin Faransa Tarel wanda ke tsare tun bayan marin shugaba Macron tafi a ranar Talata, ka iya fuskantar hukuncin daurin shekaru 3 da kuma biyan tarar euro dubu 45 bisa laifin da ya aikata na cin zarafin mai rike da babban mukamin shugabancin al’umma da gangan.

Masu bincike sun ce Damien da aka bayyana da maras hayaniya a tsakanin abokan zamansa, ya shaida musu cewar, ya mari shugaba Macron ne don nuna fushinsa kan wasu manufofin shugaban ba tare da yayi tunanin abinda zai biyo baya ba.

Shugaban Faransa Emmanuel Macron cikin jama'a a birnin Valence dake kudu maso gabashin kasar Faransa, inda wani matashi ya mare shi a bainar jama'a.
Shugaban Faransa Emmanuel Macron cikin jama'a a birnin Valence dake kudu maso gabashin kasar Faransa, inda wani matashi ya mare shi a bainar jama'a. AP - Philippe Desmazes

A nasa bangaren duk da tafin da ya sha, shugaba Emmanuel Macron ya sha alwashin cigaba da gaisawa da jama’a, a yanayin da masana suka ce yana sharar fagen sake tsayawa takara ne a zaben shugabancin Faransa dake tafe shekarar 2022 dake tafe.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.