Canada - Venezuela

Canada na neman fiye da dala biliyan 1 don tallafawa a 'yan Venezuela

Wasu 'yan gudun hijira da suka tsere daga Venezuela a yayin da suke kokarin tsallakawa cikin kasar Amurka ta yankin Rio Grande.
Wasu 'yan gudun hijira da suka tsere daga Venezuela a yayin da suke kokarin tsallakawa cikin kasar Amurka ta yankin Rio Grande. © REUTERS/James Breeden

Gwamnatin Canada da hukumar kula da ‘yan gudun hijira da majalisar dinkin duniya UNHCR sun ce akwai bukatar gaggawa ta neman tara kusan dala biliyan 1 da rabi domin tallafawa ‘yan gudun hijirar Venezuela da suka tserewa rikicin siyasa da na tattalin arzikin kasar.

Talla

Sanarwar Canadan da kuma hukumar UNHCR kan neman tallafin ta zo ne gabannin taron kafa gidauniyar agazawa dubban ‘yan Venezuelan da zai gudana a birnin Ottawa ranar 17 ga watan Yuni.

Kididdiga ta nuna cewar ‘yan Venezuela akalla miliyan 6 ne suka fice daga kasar babu shiri, sakamakon matsin tattalin arziki, da kuma rikicin siyasar da ya dabaibaye su, lamurran da suka tilasta musu shafe dubban kilomitoci suna tafiya a kasa, kafin isa wasu kasashen yankin Latin da na Caribbean.

Venezuela da kawo yanzu ta shafe shekaru 8 cikin matsin tattalin arziki ta fada rikicin siyasa ne a watan Janairun 2019, lokacin da jagoran ‘yan adawa Juan Guaido kuma kakakin majalisar dokokin kasar, yayi shelar ayyana kansa a matsayin halstaccen shugaban kasar ta Venezuela.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.